Kana da Bege da kuma Gobe

Kana da Bege da kuma Gobe

Irmiya 29:11: “Gama na san irin shirin da nayi maku” ni Ubangiji na fada. “Shirin alheri, ba na mugunta ba. Zan baku gabata da sa zuciya”. Ba abin kwanciyar hankali bane sanin akwai shiri ga rayuwarka? Ko da menene ya faru akan hanya, ko da wadanne cikas da tuntube marasa kyau, Allah yana biyo da kai ga wannan lokacin. A gaskiya, Yana ta biyo da kai gare Shi. Gaskiyar al’amarin shi ne begenka da gobenka duka suna cikin Shi ne.

Wancan na nufin, zaka iya rayuwarka duka tare da, kuma domin Yesu. Kuma saboda Shi, saboda alkawarinsa na bazai taba barinka ko yashe ka ba, yanzu kana da wani abinda zaka yi murna kwarai akai!

Tafiya ne: Tsari ne na tsawon rayuwa
Zaka na tambayan kanka, menene zan yi yanzu da na karbi Kristi? Babban tambaya ne tunda ka dauki taku na farko. Ko da yake zai yiwu baka ji wani bambanci yau ba, ka sani cewa Kristi ya fara aiki a cikinka.

Kolosiyawa 2:6-7 yace, “Da yake kun yi na’am da Almasihu Yesu Ubangiji, to sai ku tsaya gare shi. Kuna kafaffu, kuna ginuwa a cikinsa, kuna tsayawa da bangaskiya gaba-gaba, dadai yadda aka koya maku, kuna gode wa Allah ko yaushe” Wadannan tushen na kafuwa ne akan hanya ta wurin adu’a, karatun maganar Allah, wato Bible, da barin Ruhu mai Tsarki ya bi da kai da yi maka jagora.

Fara yin Rayuwarka da Kristi
Alkawari na maganar Allah, da maganan da Yesu yayi wa Almajiransa su ne wannan: Barawo yakan zo ne kawai don sata, da kisa da hallakarwa. Ni kuwa na zo ne domin su sami rai, su kuma same shi a yalwace. – Yahaya 10:10

An kiraye ka kayi cikakken rayuwa mai dadi cikin Kristi kuma muna so mu taimakeka ka fara tafiyarka da karfi.

Facebook icon Twitter icon Instagram icon Pinterest icon Google+ icon YouTube icon LinkedIn icon Contact icon