BEGE DOMIN MAWUYACIN LOKUTA
Mai yiwuwa kana fama da wani masifar da ba a yi tsammani ba, kuma baka da tabbacin yadda zaka farfado ka ci gaba. Ko mai yiwuwa kana shan wahala da wani rashin lafiya kuma baka da hanyar ganin likita. Na sani cewa mutane dayawa na rayuwa yau da kullum, basu da tabbacin daga ina abincinsu na anjima zai fito.
Sa’anda muke fuskantar wani abu mai tsananin wahala, muna iya jarabtuwa mu bari mu kuma fasa. Amma dai, Abu daya mafi girma da zamu iya yi shi ne mu kafa amincinmu ga Allah mu kasance cike da bege. Amma a gakiya, menene bege?
Bege shi ne sa rai cikin karfin hali cewa wani abu mai kyau zai faru. Yana da dangantaka mai kusanci da bangaskiyarmuda abinda muka gaskanta. Sa’anda muka yi niyar kafa bege, yana cika
rayuwarmu da farinciki da salama.
Magabci yana so mu kasance da rashin bege. Yana so ya sa mu yarda cewa mun rasa komai kuma babu abinda zai taba yin kyau.
Amma Allah yana so mu kasance cike da bege-muna gaskanta da sa rai ga manyan abubuwa daga gare Shi. A gaskiya, Littafi Mai Tsarki ya ce Shi ne “Allah na bege,” cike da jinkai da sabon mafari
(duba Romawa 15:23).