Sa’anda ka koyi yadda zaka san Yesu, ka fara sabon tafiya mai ban mamaki zuwa ga shirin Allah ga rayuwarka. Romawa 3:23 ya fade shi haka: Gama dukanmu mun yi zunubi, kuma mun kasa ga daukakar Allah. Sanin Yesu shi ne amincewa kana bukatan shi, Gaskantawa da abinda yayi maka da karban kyautarsa mai ban mamaki. Yana tabbatar da cewa baza ka iya yin rayuwan nan da kanka ba, cewa kayi zunubi kuma kana bukatan mai ceto.
Kuma labari mai dadi game da sanin Yesu , game da samun ceto, shi ne kyakkyawan musanya da ke faruwa a wancan lokacin. Kana ba shi dukan munanan abubuwa na zunubi da ka yi, don haka kuma, Allah zai baka komai da ya tanada gareka. Ko ka sani ko baka sani ba tukunna, Shirin sa domin rayuwarka yana da ban mamaki, kuma wannan ne farkon taku ga wancan tafiyar.